Gagarumar guguwa ta fada wa India

mahaukaciyar guguwa da ruwa a India
Image caption rahotannin farko sun ce guguwar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla biyar

Wata mahaukaciyar guguwa mai tafe da ruwa ta yi kaca kaca da itatuwa da hanyoyin wutar lantarki a yankunan da ke gabashin India.

Rahotanni sun ce karfin iskar da ke kadawa ya kai na gudun kilomita 200 cikin sa'a guda.

A kalla mutane biyar ne aka bayyana cewa sun mutu a lamarin yayin da kuma hukumomi suka ce sun kwashe mutane fiye da dubu 500 zuwa wasu yankunan mun tsira a Jihohin Orissa da kuma Adhra Pradesh.

Tun da farko dai hukumomin kasar India sun gargadi jama'a da cewa su yi taka tsan-tsan-tsan ganin irin mummunan hadarin da ke fuskantar wasu sassa na jihar Orissa inda suka bukaci al'ummomin da ke zaune a yankunan da su gaggauta ficewa daga gidajensu.

Kawo yanzu mutane fiye da dubu 440 ne suka fice daga muhallansu domin tserewa mahaukaciyar guguwar ta Phailin a mashigin ruwan Bengal.

Sai dai gabannin isowar guguwar, jami'ai sun ce sun shirya tsaf don tunkarar wannan bala'i.

A shekarar 1999 irin wannan iska mai karfi, ta hallaka mutane fiye da dubu goma a jahar Orissa.