Jirgin IRS ya yi saukar gaggawa a Kaduna

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya wasu fasinjojin jirgin sama su kimanin 90 suka tsallake rijiya da baya bayan da jirgin da suke ciki na kamfanin IRS ya sami matsalar taya da kuma birki yayin da yake kokarin sauka a kaduna.

Rahotannin sun ce jirgin wanda ya taso daga Lagos zuwa kaduna yayi ta shawagi a sararin samaniya sanadiyyar matsalar har zuwa lokacin da aka yi masa tanadin saukar gaggawa.

Wannan lamari dai ya sake tado da batun matsalar hadarin jiragen sama a Najeriya, wanda ke neman zama ruwan dare a kasar.

Wasu daga cikin fasinjojin jirgin sun yi kira ga hukumar kula da zirga zirgar jirage ta Najeriya ta sa ido wajen tabbatar da lafiyar jirage domin kare rayuwar jama'a.

Karin bayani