An sace ma'aikatan Red Cross a Syria

Ma'aikatan kungiyar bada agaji ta duniya Red Cross
Image caption Ma'aikatan kungiyar bada agaji ta duniya Red Cross

Kungiyar agaji ta duniya Red Cross ta ce an sace ma'aikatanta su bakwai a arewa maso yammacin Syria.

Wata mai magana da yawun kungiyar a Damascus Rima Kamal ta shaidawa BBC cewa ma'aikatan kungiyar su shidda da kuma wani ma'aiakacin sa kai a kungiyar agaji ta Red Crescent na Syria an ritsa su da bakin bindiga aka kuma yi awon gaba da su a kusa da garin Saraqeb a gundumar Idlib.

Ta ce tawagar ma'aikatan suna kan hanyar su ce ta komawa Damascus a yau a motarsu da aka zana tambarin Red Cross balobalo a jikinta.

Karin bayani