Bankin duniya ya yi gargadi

shugaban bankin duniya Jim Yong Kim
Image caption Mr Kim ya ce su kansu kasashen da suka ci gaba abin zai juyo ya shafe su

Bankin Duniya ya yi gargadin cewa tattalin arzikin duniya zai gamu da gagarumar matsala.

Idan 'yan siyasa a Amurka suka kasa kara yawan ikon da gwamnati ke da shi na cin bashi.

Shugaban bankin Jim Yong Kim, ya ce akwai hadarin tashin yawan kudin ruwa da kuma takaitar ci gaba ta tattalinarziki.

Mr Kim ya bayyana hakan ne a karshen taron shekara shekara na bankin duniyar da kuma Asusun bayar da lamuni na duniya a Washington.