Macen da ta taba takarar shugaban kasa a Nijar

Madam Bayar Mariama Gamatche
Image caption Madam Bayar Mariama Gamatche

A Jamhuriyar Nijar mun tattauna da macen farko da ta taba yin takarar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2011.

Madam Bayar Mariama Gamatche ta taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar da kungiyoyin matan Nijar suka yi, domin neman karin 'yanci.

Haka kuma ta jagoranci zanga-zangar da mata suka yi a ranar 13 ga watan Mayu na 1991, domin neman a dama da su a ayyukan babban taro na kasa.

Tun daga lokacin ne hukumomin Nijar suka ware ranar 13 ga watan Mayu na kowace shekara, ta zama Ranar tunawa da matan kasar.

Madam Bayar ta na ganin mata a Nijar sun fara samu wani cigaba, wajen kulawa da hakokin mata a matsayin 'yan kasa. tun bayan boren.

Sai dai ta ce batun rashin adalci abu ne dake cigaba da ciwa matan kasar tuwo a kwarya.