Sauyi a rayuwar matan Rwanda

Victoire Ingabire wata 'yar kabilar Hutu da ta yi takarar shugabancin Rwanda
Image caption Victoire Ingabire wata 'yar kabilar Hutu da ta yi takarar shugabancin Rwanda

Shekaru masu yawa da suka wuce, ana danganta mata da rauni a kasar Ruwanda, saboda matsaloli na rashin basu hakkokinsu sabanin yadda ake baiwa maza.

Sai dai al'amura sun fara sauyawa a yanzu, mata a kasar na cigaba da shiga bangarori dabam-dabam, da suka hada da siyasa da kimiyya da fasahar sadarwa da kuma sauran al'amura da suka shafi cigaban rayuwar bil' adama.

A halin yanzu mata a Rwanda ne ke rike da kashi 64 na kujerun majalisar zartarwar kasar, kuma suke da rinjaye.

Wasu dalibai mata 45 dake koyon darasin kimiyyar halittar dan Adam wato Biology, a makarantar 'yan mata ta Fawe dake birnin Kigali, sun bayyana gamsuwa da jindadi kan darasin da ake karantar da su na kwayoyoyin haihuwa na mace.

Helene Nomugisha na daya daga cikin daliban ta bayyana burinta na son zama likita mai aikin tiyata.

Helene ta samu dama wanda takwarorinta mata a shekarun baya basu samu irinta ba, na shiga makaranta da zabar irin fannin da suke son kwarewa a kai.

Tace ba ta yi amanna da ganin da wasu mutane ke yi ba, na cewa aiki kaza ya dace da jinsi kaza.

Duk da irin nasarorin da Rwanda ta samu wajen bunkasa rayuwar mata, har yanzu akwai gagarumin gibi da kasar ke fuskanta, na karancin mata masu koyarwa a manyan makarantu, da karancin likitoci mata da kuma injiniyoyi.