Iyaye na so a bayyana wadanda aka kashe a Apo

Wasu dakarun sojin najeriya
Image caption Sojojin Najeriya da hadin gwiwar jami'an SSS ne suka kai samamen na Apo a Abuja

A Najeriya, iyaye da 'yan uwan mutanen da aka kashe da wadanda suka jikkata a wani gida da ba a kammala ba dake kusa da rukunin gidajen 'yan majalisa a Abuja, sun nemi gwamnati ta bayyana sunayen wadanda abin ya shafa.

Haka kuma iyayen wadanda har yanzu jami'an tsaro ke tsare da su, suna cikin fargaba game da makomar 'ya'yansu.

Onorable Ashiru Tukur Idris na daga cikin 'yan majalisar dokokin kasar dake wakilitar yankunan wadanda abin ya shafa, kuma ya shaida wa BBC cewa, jami'an tsaro sun hana su gana wa da wadanda ake tsare da su.

Mutane dai na dakon rahoton hukumar kare hakkin dan adam ta kasar, dake bincike a kan lamarin da kuma rahoton kwamitin majalisar dattawan kasar.

Kimanin mutane 9 ne rahotanni suka ce an kashe a unguwar ta Apo, bayan wadanda aka jikkata da harbin bindiga, da kuma wasu da aka yi awon-gaba da su.