Wata matar aure ta shirya sace kanta da kanta a jihar Enugu

Matar da ake zargi da shirya satar kanta da kanta a Enugu
Image caption Matsalar satar mutane domin kudin fansa ta zama ruwan dare a kudancin Najeriya

A Najeriya, satar mutane a yi garkuwa da su bisa neman kudin fansa, tana ci gaba da daukar sabon salo a yankin kudu maso gabashin kasar.

Har ma rundunar 'yan sandan jihar Enugu ta damke wata matar aure, bisa zargin shirya sace kanta da kanta da ta yi, kuma ta nemi mijinta ya biya kudin fansa kafin a sako ta.

Matar mai suna Nancy Chucku, tana zaune ne a yankin karamar Hukumar Ogu dake jihar Enugu, kuma ana zarginta ne da hadi baki da wani dan Acaba domin samun kudin fansar daga hannun mijinta.

Satar mutane don neman kudin fansa dai ta zama ruwan dare a Najeriya, musamman ma a kudancin kasar, kuma babu alamun samun saukin matsalar.

A kwanan baya ma, wani matashi a yankin Kudu maso Gabashin Najeriyar ya hada baki da wata mata domin shirya sace kansa da kansa, inda matar ta fadawa danginsa cewa wadanda suka yi garkuwa da shi suna a biya su kudin fansa kafin su sako shi.

Har ma danginsa sun fara zuba kudin a asusun ajiyar matar da suka hada baki da matashin, amma daga bisani 'yan sanda sun bankado shirin, suka kuma cafke su.