An kai hari a ofishin 'yan sandan Makarfi

Wasu 'yan sandan Najeriya
Image caption 'Yan sanda masu sunturi sun je Makarfi, a lokacin da maharan ke kai harin

A jahar kaduna dake Najeriya wasu mahara da ba a san ko su wanene ba, sun kai hari a garin makarfi dake jahar.

'Yan bindigar wadanda rahotanni ke cewa sun zarta 50, sun yi raga-raga da bankin Keystone da kuma ofishin 'yan sanda na garin.

Amma bayanai sun nuna cewa ba su sami nasarar kwashe kudin bankin ba, a harin na ranar Lahadi da daddare.

Hukumomi dai sun ce ba a samu asarar rayuka ko jikkata ba, a lokacin artabun tsakanin maharan da jami'an tsaro.

Mazauna garin na cigaba da zaman zullumi, duk da cewa hankula sun fara kwanciya.