Babu wanda ya ci kyautar Mo Ibrahim

Mo Ibrahim
Image caption Mo Ibrahim, wani attajirin dan kasuwa ne dan kasar Sudan

A bana babu mutumin da ya lashe kyauta mafi tsoka da aka taba warewa, wato kyautar Mo Ibrahim ta shugabanci nagari a nahiyar Afrika.

Wannan shi ne karo na hudu, tun bayan bullo da kyautar a shekaru 7 da suka wuce, da kwamitin ba da kyautar ya ce babu wanda ya cancanci samun kyautar ta dala miliyan 5, da ake baiwa shugaban wata kasar Afrika da aka zaba ta hanyar dimokradiyya, kuma ya bar mulki bisa radin kansa.

Matakin ya zo daidai da lokacin da gidauniyar Mo Ibrahim ta fitar da rahoto kan shugabanci na gari a Afrika, wanda ya ce galibi an samu cigaba da kyautatuwar al'amura a kasashen Afrika, tun farkon karnin da muke ciki.

Sai dai rahoton ya nuna cewa akwai wasu fannonin da aka samu ci baya, kamar fannin doka da oda.