Musulmi na bukukuwan babbar Sallah

A yau ne al'ummar musulmi a fadin duniya ke fara bukukuwan babbar Sallah.

Bukukuwan dai sun biyo bayan kammala tsayuwar Arfat ne da mahajjata suka yi a ranar litinin wadda ita ce kololuwar ibadar ta aikin Hajji.

Daya daga cikin muhimman abubuwan da a kan gabatar a wannan lokaci na babbar Sallah shi ne yankan dabbobi bayan saukowa daga Sallar Idi.

Hakan ne ma ya sa ake kiran sallar da sallar layya.

Sai dai yayin da musulmai a duniya da ba su je aikin Hajjin bana ba ke yanka dabbobinsu na layya a yau, wasu kuwa ba za su samu damar yankan ba sabo da rashin hali da kuma tsadar dabbobi.

A irin wannan yanayi wasu masu karamin karfi kan yanke shawarar hada kudi da sayen dabba daya domin su yi layya, hadakar da ake cewa Watanda.

Jama'a da dama ne a Najeriya da Nijar da wasu kasashen duniya ke kokawa dangane da tashin farashin raguna da sauran dabbobi da ake amfani da su domin yin layya.

Karin bayani