Afghanistan: An kashe wani gwamna

marigayi Arsala Jamal
Image caption Ya taba rike mukamin gwamnan lardin Khost

An kashe gwamnan lardin Logar da ke gabashin Afghanistan, Arsala Jamal a wani harin bam da aka ɗana a wani masallaci lokacin sallar Idi.

Gwamnan yana gaban masallacin ne inda yake gaisawa da jama'a bayan sallar da al'ummar musulmi ke yi a yau.

Wani bam da aka ɓoye ne a ƙarƙashin wani tebur a masallacin ya tashi ya kuma kashe shi nan take.

Mai magana da yawunsa ya ce, wasu mutanen da dama sun samu munanan raunuka a harin.

A watan Afrilu aka nada Arsala Jamal a matsayin gwamnan lardin bayan ya dawo Afghanistan daga Canada.