'An kashe 'yan Boko Haram 40'

Rundunar sojan Nijeriya ta ce ta kashe mayakan kungiyar Boko Haram su arba'in, yayin da take kare wasu hare-hare da suka tsara kaiwa a lokaci guda, a jihar Borno.

Babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da labarin artabun, wanda ake kyautata zaton ya auku ranar Lahadi.

Masu aiko da rahotanni na cewa rundunar sojan a koda yaushe kan nuna cewa an kashe 'yan bindigar a lokacin gumurzun.

Amma kungiyoyin kare hakkin jama'a na cewa akwai mayakan kungiyar da ake kashewa a inda ake tsare da su.