Guguwa da ruwa sun hallaka mutane a Japan

Gugwa mai tafe da ruwa a Japan
Image caption Masu aikin ceto na gamuwa da matsaloli saboda lalacewar hanyoyi da sauransu

Akalla mutane 13 suka mutu wasu arba'in kuma suka bata a Japan sakamakon ambaliya da zaftarewar kasa da gagarumin ruwan sama da iska suka haddasa.

Guguwar mai ruwa da ba a taba ganin kamarta ba cikin shekaru a kasar da aka yi wa lakabi da Wipha ta nufi cibiyar nukiliya ta kasar ta Fukushima wadda da ta lalace.

Masu kula da cibiyar sun shiga aikin zuke ruwan saman da ke zuba a wurin domin kare aukuwar karin ambaliya.

Iska da ruwan sun kawo cikas ga harkokin sufuri a fadin kasar,

Galibin mace macen an yi su ne a tsibirin Oshima da ke kudu da babban birnin kasar Tokyo, inda ambaliya ta yi awon gaba da gidaje.