Za a mayar da Ibori zaman jarun a Najeriya

Image caption James Ibori ya sace dubban miliyoyi mallakar jihar Delta

Rahotanni a Birtaniya na nuna cewa, za'a mayar da James Ibori tsohon gwamnan Jihar Delta dake zaman jarun a Birtaniya tare da wasu fursunonin 266 zuwa gida domin su karasa zaman su na gidan kaso a can Najeriya.

Wata kotu ce dai ta yanke wa James Ibori hukuncin daurin shekaru 13 a gidan kaso a nan Birtaniya saboda samunsa da laifin barnata dukiyar jama'a.

Sai dai rahoton ya ce har yanzu ana ci gaba da tattaunawa a kan yarjejeniyar tilasta mayar da fursunonin gida don karasa zamansu na gidan kaso a Najeriya.

Minista mai kula da gidajen yari na Birtaniya Jeremy Wright, ya ce dole ne karin fursunoni 'yan kasashen waje su karasa zaman jarun dinsu a kasashensu.

Gwamnatin Birtaniya na kashe wa kowane fursuna kusan Fam dubu 40 a kowace shekara.

Karin bayani