Kwamitin Boko Haram na gab da kammala aikinsa

Boko Haram Najeriya
Image caption Boko Haram Najeriya

A Najeriya, kwamitin da shugaban kasar ya kafa don sulhuntawa da kawo karshen rikicin Boko Haram ya ce yana gab da gabatar da rahotonsa.

A yankin arewa-maso-gabashin kasar ne rikicin ya fi ta'azzara, tare da haddasa asarar rayukan jama'a da dama.

Tun da farko dai gwamnatin tarayya ta bai wa kwamitin wa'adin wata uku ne, amma daga bisani aka kara masa wata biyu.

Wa'adin wannan kwamiti na karewa ne a daidai lokacin da Kungiyar kare hakkin bil'adama ta amnesty International ta fitar da wani rahoto da ke zargin cewa daruruwan mutane, wadanda sojoji ke tsare da su bisa zargin alaka da kungiyar jama'atu ahlis sunnah lid da'awati wal jihad sun halaka.