Mutane miliyan 30 na cikin kangin bauta

Da sauran bayi a duniya
Image caption Da sauran bayi a duniya

Wani sabon rahoto game da bauta a fadin duniya yace kimanin mutane miliyan talatin ne ke cikin kangin bauta.

Rahoton yace kusan mutane miliyan goma sha hudu ne ke rayuwar bauta a kasar Indiya, amma matsalar tafi kamari a Mauritaniya inda kaso hudu cikin dari na al'ummar kasar bayi ne.

Nick Grono shi ne shugaban kungiyar Walk Free Foundation ta kasar Australia wacce ta wallafa rahoton.

Yace; "Har yanzu ana samun bautar gado a Mauritaniya; inda ake haifar 'ya'ya cikin bauta. Ana bautar da maza da mata tare da 'ya'yan da suka haifa, inda ake tilasta musu ayyukan gida ko kuma kiwo,wannan tshohuwar matsala ce a kasar Mauritaniya."