'Ana bukatar karin dakaru a Mali'

Dakarun Afirka a kasar Mali
Image caption Dakarun Afirka a kasar Mali

Majalisar Dinkin Duniya ta nemi karin dakaru da kayan aiki ga rundunarta ta wanzar da zaman lafiya a Mali don tabbatar da tsaro a arewacin kasar.

Wakilin majalisar a Mali, Bert Koenders ya ce wajibi ne a gaggauta karin dakaru, don hare-haren da aka kai na baya-bayan nan a arewacin kasar tamkar gargadi ne ga majalisar.

Ya kuma yi kira ga duk kasashen da ke cikin kwamitin tsaro da kuma sauran kasashen da ke bada gudunmawar soji da 'yan sanda, da su gaggauta kawo karin jami'ai domin rundunar wanzar da zaman lafiya a Mali ta sauke nauyin da aka dora mata.

Adadin dakarun rundunar majalisar a Mali ya gaza rabin jami'ai dubu goma sha biyun da aka shirya kai wa, sannan rundunar ta kara samun nakasu bayan da Najeriya ta janye tawagarta a watan Agusta domin tunkarar kalubalen tsaron da ta ke fuskanta na cikin gida.