An bude ma'aikatun gwamnati a Amurka

Barak Obama
Image caption Barak Obama

Bayan shafe makonni biyu ana dauki ba dadi, an bude ma'aikatun gwamnatin Amurka tare da kaucewa barazanar kasa biyan basussukan da ake bin kasar a kan kari.

Shugaba Obama ya rattaba hannu kan dokar bayanda Majalisar Dokoki ta zartar da kudirin.

Majalisar dattawa ta zartar da kudirin dokar da gagarumin rinjaye, yayinda majalisar wakilai ta zartar da ita da kyar da jibin goshi, bayanda 'yan jam'iyyar Republican mai adawa su ka soki kudirin.

Sun soki dokar ne da gaza cimma bukatunsu musamman ma dakile dokar samar da kiwon lafiya ga talakawan kasar da shugaba Obama ya kawo.

A nasa bangare, shugaba Obama yace ya na fatan hakan zai kawo karshen abinda ya kira gudanar da mulki ta hanyar rikici, inda ya bukaci 'yan jam'iyyun Democrat da Republican su mai da hankali wurin inganta rayuwar Amurkawa.

Sai dai wakilin BBC yace yarjejeniyar ta yau mai gajeren zango ce domin sai 'yan siyasa sun sake tattaunawa game da ita a farkon shekarar badi.