Tamowa ta hallaka yara da dama a Nijar a bana

Image caption Nijar ta sha fama da matsalar karancin abinci

A jamhuriyar Nijar yara 'yan kasa da shekaru biyar da haihuwa sama da 2500 ne suka rasa rayukansu cikin watanni takwas na bana sakamakon kamuwa da tamowa.

Da dama daga cikin yaran dai ba su wuce shekaru biyu da haihuwa ba.

Ofishin kungiyar UNICEF reshen Nijar ne ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Sai dai kuma har yanzu kuma hukumomin Nijar ba su ce komai ba dangane da wannan batu.