Najeriya ce ta 4 wajen bauta a duniya

Wasu yara na aiki a gonar koko
Image caption Duk da dumbin arzikin da Najeriya ke da shi, mafi yawan al'ummarta na cikin kangin talauci

Wani sabon rahoto kan bauta da wata kungiya ta 'Walk free foundation' ta fitar, ya ce Najeriya ce ta hudu a duniya da al'ummarta ke bauta.

Kungiyar wacce ke da goyon bayan tsohuwar sakatariyar wajen Amurka, Hillary Clinton da tsohon firai ministan Birtaniya, Tony Blair da hamshakin maikudin nan Bill Gates, ta kiyasa mutane 670,000 zuwa 701,032 ne ke ayyukan bauta a Najeriya.

Kasashen Mauritania da Haiti da Pakistan da su ne kan gaba a bautar da ake yi ta zamani, kana Ivory Coast da Gambia ma na cikin jerin 10 na farko.

Bauta ta zamani dai ta kunshi auren dole da ci da gumin yara da sa yara aikin karfi da sauransu.