UN: An zabi Najeriya a kwamiti tsaro

Image caption Goodluck Jonathan

An zabi Najeriya da Saudia Arabia da kuma Chadi a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a wa'adi na shekaru biyu.

Haka kuma kasashen Chile da Lithuania suma sun samu shiga cikin kwamitin sulhu mai wakilai 15.

A ranar Alhamis ne aka zabi kasashen lokacin taron kasashe mambobin majalisar dinkin duniya.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya bayyana jin dadinsa game da zaben kasar cikin kwamitin.

Kasashe biyar masu karfin fada aji na kwamitin sulhun sune; United States, Birtaniya, Faransa, Rasha da kuma China.

Karin bayani