Mauritania ce kan gaba wajen bauta

Image caption Miliyoyin jama'a ne ake bautar dasu a kasashensu.

Wani sabon rahoto game da bauta a fadin duniya yace kimanin mutane miliyan talatin ne ke cikin kangin bauta.

Rahoton yace kusan mutane miliyan goma sha hudu ne ke rayuwar bauta a kasar Indiya, amma matsalar tafi kamari a Mauritaniya inda kaso hudu cikin dari na al'ummar kasar bayi ne.

Nick Grono shi ne shugaban kungiyar Walk Free Foundation ta kasar Australia wacce ta wallafa rahoton.

Yace "Har yanzu ana samun bautar gado a Mauritania, inda ake haifar 'ya'ya cikin bauta. Ana bautar da maza da mata tare da 'ya'yan da suka haifa, inda ake tilasta musu ayyukan gida ko kuma kiwo,wannan tshohuwar matsala ce a kasar Mauritania."

Kiyasin yawan bayi:

India - 13,956,010 China - 2,949,243 Pakistan - 2,127,132 Nigeria - 701,032 Ethiopia - 651,110 Russia - 516,217 Thailand - 472,811 DR Congo - 462,327 Burma - 384,037 Bangladesh - 343,192