Al-Shabaab ta gargadi musulmin Birtaniya

Image caption Mayakan Al-Shabab

Kungiyar Al Shabaab ta masu kaifin kishin Islama a Somalia ta-ja kunnen musulmin Birtaniya masu sukar tsatsauran ra'ayin addini cewa, za a iya kai musu hari.

'Yan sandan sbirnin London sun soma bincike a kan wani sakon bidiyo da kungiyar Al-Shabaab ta fitar wanda a cikinsa aka ambato sunayen wasu musulmi a Birtaniya dake sukar masu ikirarin yin jihardi.

Sakon bidiyon kuma ya yaba kisan da aka yi wa sojan Birtaniya, Lee Rigby a unguwar Woolwich.

Tuni dai 'yan sanda suka soma bada kariya ga wani fitaccen musulmi dake sharhi a kan al'amuran yau da kullmu, Mohammed Ansar.

Karin bayani