'Shigar da kara kotu a kan Minista Stella'

Image caption Ministar Sufurin jiragen sama, Stella Oduah

Wata kungiyar dake ikirarin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya wato Anti-Corruption Network, ta ce za ta gabatar da ministar harkokin sufurin jiragen saman Najeriya, Misis Stella Oduah gaban kuliya idan har taki yin murabus.

A cewar kungiyar, Ministar ta saba dokar gwamnatin saboda sayar mata wasu motocin kawa kirar BMW a kan fiye da naira miliyan 200.

Shugaban kungiyar Anti Corruption Network, Mr Dino Melaye yace " dokar Najeriya ta hana a siyarwa ministoci motoci sannan kuma an tsugawa motocin kudi".

Melaye yace" idan zuwa ranar Talata ministar bata yi murabus ba, za su gudanar da zanga-zanga".

Kafofin yada labaran Najeriya sun ambato, kakakin ministar, Joe Obi yana cewar an sayi motocinne don kare lafiyar ministar daga duk wata barazana.