Mage na fasakwaurin wiwi a kurkuku

Wata mage
Image caption A Brazil a farkon shekarar nan ma an kama wata mage dauke da kayayyakin da za a yi amfani da su wajen gudu daga kurkuku

Wasu ma'aikatan kurkuku a Maldova sun kama wata kyanwa da ake amfani da ita wajen fasakwaurin tabar wiwi.

Yawan shiga da fitan da magen ke yi ta wani rami a katangar gidan yarin ne ya ja hankalin ma'aikatan, musamman ganin yadda wuyanta ya yi kauri.

Jami'an gidan sarkar sun ce wani mutum ne dake zaune a kauyen Pruncul ke amfani da magen, wajen safarar tabar wiwin zuwa gidan mazan.

A watan yunin da ya gabata ma dai masu gadi sun kama wata mage da aka daura wa wata jaka, da ta kunshi wayoyin salula a kasar Rasha.