Ma'aurata sun sayar da 'yarsu sun sayi waya

Image caption Ma'auratan sun ce suna so 'yarsu ta samu kyakkyawar rayuwa.

Kafafen watsa labarai a kasar China sun ce wasu ma'aurata za su gurfana a gaban kotu saboda zargin sayar da 'yarsu, kana suka sayi wayar salula ta iPhone da wasu kayayyakin masarufi da kudin.

Ma'auratan dai sun sanya talla a intanet, suna neman wanda zai sayi 'yar tasu a kan kudi dala 8,000 tun ma kafin a haife ta.

Bayan an haife ta ne iyayen nata suka sayar da ita kan makudan kudade.

Ma'auratan sun shaidawa 'yan sanda cewa suna son 'yar tasu --- ita ce 'ya ta uku da suka haifa --- ta samu ingantacciyar rayuwa fiye da wadda suke yi.

A bara ma dai, wani dan kasar ta China ya sayar da kodarsa, sannan ya sayi wayar iPhone da kwamfyuta ta iPad da kudin.

Karin bayani