An gano gawawwakin 'Mahara' a Kenya

Wannan hoton bidiyon ya nuna maharan dauke da bindigogi
Image caption Hoton bidiyon ya nuna maharan dauke da bindigogi, a wani shago dake rukunin shagunan na Westgate a Nairobi

Ana kyautata zaton wasu gawawwaki biyu da suka kone da aka ciro a baraguzan rukunin shaguna na Nairobi, na biyu daga cikin mahara ne, kamar yadda wani dan majalisa ya shaida wa BBC.

Ndung'u Gethenji, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisa dake bincike a kan harin na Westgate ya ce, har ila yau a ranar Alhamis an kuma gano gawar wani soja.

Za a yi gwajin kwayoyin halittar gawawwakin uku, domin tabbatar da ko su wanene.

Tun da fari wasu hotunan bidiyo na harin sun nuna daya daga cikin mutanen da ake zargi da kai hari a rukunin shagunan, wani dan kasar Norway ne mai kimanin shekaru 23.

Kungiyar Al-Shabab ta kasar Somalia ta dauki alhakin kai harin, wanda ya hallaka fiye da mutane 60.