An kashe babban jami'in tsaro a Benghazi

Image caption Akwai tabarbarewar tsaro a fadin Libya

Rahotanni daga birnin Benghazi na Libya na cewa, wasu 'yan bindiga sun hallaka babban jami'in leken asiri na 'yan sandan rundunar sojan kasar.

Jami'an tsaro sun ce, 'yan bindigar sun yi wa marigayin, Ahmed Barghathi harbi sau da dama yayin dake barin gidansa domin halartar Sallar Juma'a.

Har yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.

Masu aiko rahotanni sun ce, wannan shi ne alamar rauni na baya-bayan da gwamnatin Libya dake kokarin tsayawa akan kafafunta ta fuskanta.

Karin bayani