Najeriya: Shugaban hukumar kidaya ya yi murabus

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A Najeriya, shugaban hukumar kidayar al'umar kasar Festus Odimegwu ya yi murabus kuma gwamnatin kasar ta nada Sam Ahaiwe ya maye gurbinsa.

Tsohon shugaban hukumar kidayar jama'ar dai ya fuskanci suka daga wasu jihohin kasar, bayan wasu kalaman da ya yi cewar sakamakon kidayar da aka yi a Najeriya a baya-bayan nan na cike da kura-kurai.

Kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga ofishin sakataren gwamnatin Najeriyar ta nuna, shugaban kasar Goodluck Jonathan ya ce ya amince da murabus din da shugaban hukumar ta kidaya ya yi.

Duk da cewa babu wani dalili da gwamnati ta bayar game da murabus din Mr Odumegwu, wasu na zargin ba za ta rasa nasaba da takaddamar da ya fada bayan wasu kalaman da ya yi cewa rabon Najeriya da yin kidaya mai inganci tun a shekarar 1816.

Mr Odumegwu ya kuma zargi 'yan siyasa da kambama sakamakon kidayar don cimma wata manufa ta siyasa.