'Barci na wanke dafin dake kwakwalwa'

Image caption Mutum na bukatar barci don kwakwalwa tayi aiki da kyau

Masu bincike a kasar Amurka sun ce sun gano daya daga cikin manyan dalilan da suka sa ake yin barci.

Masana kimiyya a jami'ar Rochester sun ce gwajin da suka yi a kan beraye, ya nuna cewa kwakwalwa na amfani da bacci ne wurin wanke dafin da ke taruwa a cikinta lokacin da dabbobi ke ido biyu.

Jagorar masu binciken Maiken Nedergaard, ta ce kwakwalwa kamar mai masaukin liyafa ce; ko dai ta yi maraba da baki ko ta share kazantar da suka tara amma dai ba za ta iya ayyukan biyu a lokaci guda ba.

Nedergaard tace " Ina ga duk mun san bacci na da amfani amma ba ma son yin sa, musamman ma kananan yara, ga dabbobi kuma bacci abu ne mai hatsari domin za'a fi saurin farautarsu idan su na cikinsa".

Binciken ya gano cewa ana tsaftace kwakwalwa da kyau cikin barci fiye da a farke.

Karin bayani