Ba mu samu korafi daga Saudiyya ba —Ban Ki Moon

Image caption Ban Ki-moon ya ce wasu kasashe suna tattaunawa a kan matakin da Saudiyya ta dauka

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce kasar Saudiyya ba ta aike masa da sakon kin amincewa da zama mambar wucin-gadi ta Kwamitin Sulhu na majalisar ba.

Mista Ban ya ki ya tabbatar ko ya musanta cewa zai kira Sarkin Saudiyya domin tattaunawa game da batun.

Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar ya ce ya fahimci cewa wasu kasashe mambobin Kwamitin Sulhun suna tattaunawa da junansu game da batun.

Tun da farko dai kasar ta Saudiyya ta ki amincewa da kasancewa mambar Kwamitin Sulhu na Majalisar, tana mai zargin majalisar da rashin katabus wajen warware rikice-rikicen da ke faruwa a duniya.

Karin bayani