Tsagaita wuta domin taimakon jin kai a Syria

  • 19 Oktoba 2013
Babbar Jami'ar ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya
Babbar Jami'ar ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniyar dai ta yi kira a tsagaita wuta nan take a lardin Moedamiyat al Sham domin baiwa hukumomin gaji damar kai magunguna da kayayyakin taimakon jin kai ga jama'a fararen hula.

An kwashe dubban mutane a ranar Lahadin da ta wuce wadanda suka hada da mata da yara kanana da kuma tsofaffi, to amma har yanzu akwai yawan wannan adadi na jama'ar da basu sami damar barin wannan yanki na yan tawaye da aka yiwa kawanya ba saboda ci gaba da barin wuta da ake yi.

Hukumomin gaji su na kokarin kaiwa jama'a dauki to amma suna fuskantar matsaloli masu yawa.

Simon Shorno mai magana da yawun kungiyar agaji ta Red Cross a Damascus ya baiyana cewa

"Wannan matsanancin yanayi ne hakika, na farko ga dukkan mutanen da yakin da kuma killacewar ta ritsa da su.To amma ga kungiyoyin agaji kamar Red Crossa da kuma Red Crescent ta Siriya, muna bukatar tattaunawa da gwamnati domin samun damar kai kayan agaji ga wadannan wurare."

Tsawon watanni dai kenan rabon da jama'ar da wannan lamari ya ritsa dasu su sami wani nau'i na gudunmawar jin kai.

Hatta Biredi da filawa ba a bari an shiga da shi yankin ba a tsawon watanni uku da suka wuce, likitoci sun ce sun sha baiyana irin matsanancin hali da galabaitar da yara ke ciki sakamakon rashin ingantaccen abinci musamman ga yara yan kasa da shekaru biyu da haihuwa.

Akwai rahotanni dake cewa ana tilastawa mutane cin naman moshen kare.

Kakakin kungiyar agajin ta Red Cross a Damascus Simon Shorno ya kara da cewa al'amarin tsaro ya kasance mai matukar wahala hatta ga ma'aikatan agaji.

Babbar jami'ar taimakon jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta baiyana matukar damuwa da halin da ake ciki a kasar Siriya baki daya.

Ta jaddada cewa wajibi ne a kyale jama'a fararen hula su fice zuwa yankunan tudun mun tsira ba tare da fargabar kai musu hari ba.

Karin bayani