'Yan Lebanon da Syria ta saka sun isa gida

Dawowar tsararrun Lebanon
Image caption Dawowar tsararrun Lebanon

'Yan kasar Lebanon guda tara da 'yan tawayen Syria suka cafke a bara sun koma Beirut bayanda aka sako su.

Iyalansu da kuma 'yan siyasar Lebanon da dama ne dai su ka tarbe su a filin jiragen sama na Beirut.

An cafke mutanen da ke ikirarin su masu ziyarar ibada ne na Shia a daura da iyakar Syria da Turkey.

An kuma sako su ne bayanda aka saki matukan jiragen sama 'yan kasar Turkey guda biyu da aka kama a Lebanon cikin watan Agusta.

Haka kuma yarjejeniyar sakin na su ta hada da sakin wadansu 'yan tawaye mata da gwamnatin Syria ta kame.