Wutar daji na yaduwa a Australia

Wutar daji a Australia
Image caption Wutar daji a Australia

Yanzu haka dai 'yan kwana-kwana a jihar New South Wales ta kasar Australia na ta dauki ba dadi na ganin sun shawo kan wutar dajin dake ci gaba da yaduwa a yankin.

Kwamishinan hukumar kwana-kwana mai lura da yankunan karkara na yankin New South Wales, Shane Fitzsimmons ya ganin yadda masana ke kyautata zaton cewa lamarin zai yi matukar muni akwai butakar jama'a su bada hadin kai.

"Ya ce muna bukatar jama'a su taimaka mana kuma su rika sa ido sosai, abun da bama fata shine yin kara ruruta wannan gobara, domin yanzu haka mun karkata hankulanmu tare da aikewa da karin jami'ai zuwa yankunan da gobarar ta yi tsanani."

Rahotanni sun ce gobarar ta fi muni ne a yankin tsaunukan Blue Mountain na yammacin Sydney inda daruruwan jama'a suka rasa muhallansu.

An kuma kafa dokar ta baci a Jihar ta New South Wales domin baiwa hukumomi karfin ikon tilastawa mutane su bar gidajensu idan hakan ya zama wajibi.

Wannan matakin dai na zuwa ne a yayin da ake gani lamarin na neman kara tabarbarewa inda Masana yanayi suka yi hasashen cewa za a sami karuwar zafi da kuma iska mai karfi wanda hakan zai sanya gobarar ta kara ruruwa cikin yan kwanaki.

Gobarar dajin ta bana dai ita ce mafi muni a cikin shekaru goma, inda tuni ta kone fiye da gidaje dari biyu.

Karin bayani