Cutar amai da gudawa ta barke a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari.
Image caption kimanin mutane hamsin gwamnatin jihar ta bayyana sun rasa rayukansu, yayin da jama'ar gari ke cewa adadin ya wuce haka.

A jahar Zamfara da ke arewacin Najeriya, ana ci gaba da samun mace-mace sakamakon cutar amai da gudawa data barke a wasu sassan jahar tun a makon jiya.

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa sama da mutane dari daya da talatin ne suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu a yankunan kananan hukumomi kimanin shida da lamarin ya shafa.

Sai dai gwamnatin jahar ta Zamfara ta ce kimanin mutane hamsin ne kawai take da masaniyar cewa sun rasa rayukarsu a cutar ta amai da gudawa data barke.

Gwamnatin Jihar ta dauki matakin bada tsaftataccen ruwan sha, tare da magunguna da ma'iakata da kayan aiki, da kuma bada kulawa ta gaggawa ga duk wanda ya kamu da wannan cuta ta amai da gudawa kyauta.