Amurka:Bankin JP Morgan zai biya tarar dala biliyan 13

Bankin JP Morgan
Image caption Bankin JP Morgan

Bankin zuba jari na JP Morgan Chase a Amurka zai biya ma'aikatar sharia fiye da dala biliyan 13 don kaucewa tuhumar da ake yi masa.

Ana tuhumar bankin ne da sayar da takardun basussuka da suka saba ka'ida tun kafin fadawar kasar cikin rikicin tattalin arziki.

Idan dai aka tabbatar da rahotannin, wannan shi ne mafi girma da wani kamfani a Amurka zai bayar domin daidaita irin wannan al'amari.

Sai dai hakan ba zai hana a fasa wani binciken aikata laifuffuka ba a bankin.