Hotunan kamfe na jihar Gombe a Saudia

Taswirar kasar Saudi Arabia
Image caption Taswirar kasar Saudi Arabia

Cece-kuce ya kunno kai game da manna hotunan kamfe na gwamnan jihar Gombe arewacin Nijeriya don neman tazarce a zaben shekara ta 2015.

An dai manna hotunan gwamna Ibrahim Dankwambo a wurare da dama a wasu birane na kasar saudiyya yayin aikin hajji.

Masu sukar matakin yakin neman zaben na gwamnan jihar ta Gombe a kasar Saudiyya dai na cewa, lika hotunan a lokacin da muliyoyin musulmi daga sassa daban-daban na duniya ke gudanar da aikin hajjin bai dace ba.

Sai dai masu goyon bayan matakin sun ce kuma ke hakan ya yi daidai, don alama ce ta nuna soyayya da kuma fayyace inda 'yan jihar ta Gombe suke.