An kai harin bam a birnin Hama na Syria

Harin bam a Hama
Image caption Harin bam a Hama

Wata motar da aka dana wa bam ta tarwatse a birnin Hama na tsakiyar Syria kuma akalla mutane talatin sun hallaka.

Kamfanin dillancin labaran Syriar ya ce, wata babbar mota ce makare da bama-baman da nauyinsu ya kai ton daya da rabi ta tarwatse a wajen birnin Hama daga gabas, a kan wata babbar hanya mai cunkoson ababen hawa.

Kamfanin dillancin labaran ya dora alhakin harin a kan 'yan ta'adda.

A cewar masu fafutuka, bam din ya tashi ne a wani wurin bincike na sojoji, kuma dayawa daga cikin mamatan sojoji ne.

Harin na yau ya faru kwana daya bayan da 'yan tawaye masu jihadi suka kai harin bam a birnin Damascus, inda sojoji akalla goma sha shidda suka rasa rayukansu.

Shugaban kungiyar kasashen Larabawa ya ce, a ranar 23 ga watan Nuwamba mai zuwa za a bude babban taro a kan Syria, wanda aka dade ana jira - ko da yake wannan ba sanarwa ba ce ta zahiri.

Nabil El-Arabi na magana ne bayan ya gana da wakilin kasashe a Syria, Lakhdar Brahimi, wanda ke rangadi a yankin gabas ta tsakiya domin shirya taron.