Tarihin Maryam Ahmed Sabo

Image caption Maryam Sabo tana fafutikar kare hakkin mata da yara

Maryam Ahmed Sabo ita ce babbar mai shari'a kuma mataimakiyar rajistara a ma'aikatar shari'a ta jihar Kano da Babbar kotun jihar.

Tana yanke hukunci a kan shari'ar da ta danganci aikata manyan laifuka da laifukan da suka shafi zamantakewa.

Mace ce da ta kware a harkokin shari'a, inda ta kwashe fiye shekaru 18 tana wannan fanni.

Ita ce mai shari'ar da ke kula da shari'ar da ta shafi laufukan da yara ke aikatawa.

Kazalika, Maryam Sabo tana fafutikar kare hakkin dan adam -- ta fi ba da muhimmanci wajen kare hakkin mata da kananan yara da bayar da shawarwari da kuma wayar da kan mata game da fyade da cin zarafin mata a jihar Kano.

Maryam Sabo ta yi karatunta na dipiloma a kan shari'ar addinin musulinci da dokokin zamantakewa, kana ta yi digiri a wannan fanni, dukka a Jami'ar Bayero da ke Kano a shekarar 1991.

Ta zama cikakkiyar lauya a shekarar 1993.

Haka kuma Maryam Sabo ita ce shugabar hadaddiyar kungiyar lauyoyi mata ta Nigeria reshen jihar Kano.