'Yan Boko Haram sun kashe mutane 19

Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

'Yan bindiga sanye da kayan soji sun kashe mutane akalla 19 a kan titi a jihar Borno dake kudu maso gabashin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewar 'yan bindigar su tsayar da motoci a kan hanya, sannan suka bukaci mutane su fito kafin su bindigesu.

Harin ya auku ne a safiyar ranar Lahadi a garin Logumani wanda ke kusada kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru.

Shaidu sun shaidawa BBC 'yan bindigar 'yan kungiyar Boko Haram ne, duk da cewar kungiyar ba ta ce komai ba game da harin.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane da dama tare da kona makarantu da wuraren ibada.

Wadanda suka tsira daga harin, sun ce 'yan Boko Haram din su yi musu kwantar baune ne a kan babura.

Karin bayani