Facebook ya dage haramcin sanya hotuna masu tada hankali

Shafin sada zumunta da muhawara wato Facebook
Image caption Shafin sada zumunta da muhawara wato Facebook

Shafin sada zumunta da muhawara wato Facebook, ya ce zai baiwa jama'a damar sanya hotunan Vidiyo na tashe-tashen hankula a shafinsa, matakin da ke nuna sauya haramci na wucin gadi da shafin ya yi a watan Mayun wannan shekarar.

Facebook ya ce zai baiwa mutane damar sanya irin wadannan hotuna ne domin su gujewa aikata su ba wai don su dauki dabi'ar yin haka ba, kuma shafin zai kara gargadin hana sanya hotunan da ke da matukar tada hankali.

Haka kuma shafin ya haramta sanya hotunan da suka shafi batsa.

Sai dai wata kungiya mai zaman kanta da ke hana aikata kisan kai da hukumar da ke sa ido kan tabbatar da tsaro a shafukan yanar gizo sun soki lamarin na facebook.