Shin ina matar Janar Murtala Muhammed?

Image caption Ajoke a cikin gonar ta

Matar tsohon shugaban gwamnatin mulkin soji a Najeriya, Ajoke Muhammad, a yanzu ta maida hankalinta ne wajen noma musamman shuka irin kwakwar manja .

A yanzu tafi kowa yawan itatuwa a wajen guda a Najeriya, inda take da bishoyoyi iri-iri na abubuwa daban daban fiye da 2,000 sannan kuma ga irin kwakwar manja daban-daban guda 400 da ta shuka a gonarta a Abuja cikin shekaru takwas.

'Yar shekaru 72, Ajoke na shigo da irin ne daga wasu kasashen duniya, don tabbatar da cewar ba a daina shuka kwakwar manja ba.

Tace" Ina baiwa shuka mahimanci saboda suna gyara muhalli".

'Rashin maida hankali'

Image caption Akwai shukar kwakwan manja da dama a cikin gonar

A lokacin turawan mulkin mallaka, Najeriya ce kan gaba a duniya wajen samar da manja.

A shekarar 1870, turawan mulkin mallaka sun dauki irin kwakwar manja daga Najeriya zuwa kasar Malaysia, kuma a yau, Malaysia ce kasar da ta fi kowacce samar da manja a duniya.

Manjar da ake samu daga Malaysia da kuma Indonesia sun fi yawan wanda ake samu a daukin nahiyar Afrika.

Najeriya ta kawar da kanta daga batun manja ne tun bayan da ta samu bullar danyen man fetur.

Misis Ajoke ta nuna takaicinta game da wannan abu da ya faru da Najeriya, inda tace 'yan kasar ba sa maida hankali wajen habbaka noman kwakwar manja.