'Yan Darika da Izala sun gana a Saudiyya

Image caption Sheikh Tijjani Bala Kalarawi

Manyan malaman musulunci na darikun Izala da Tijjaniya da kuma Kadiriyya na Najeriya, sun gudanar da taron hadaka a kasar Saudiyya.

Sun yi ganawar ce a lokacin aikin Hajin da aka kammala, da zummar samun karin hadin kai da fahimtar juna a tsakanin mabiya darikun, da kuma wanzar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya.

A wajen taron, sun amince a zauna lafiya tsakanin mabiya kowacce darika ba tare da yin batanci ba.

Sakataren kungiyar fityanul Islama ta kasa, Sheikh Tijjani Bala Kalarawi, ya shaidawa BBC cewar " mun fahimci duk da irin wa'azin batanci da ake yi, har yanzu babu wanda ya bar akidarsa".

A cewarsa, sun yi Sallah da dawafi tare a Saudi Arabia, kuma sun amince za a cigaba da zaman lafiya tsakanin mabiya akidun daban-daban na Najeriya

Karin bayani