Brunei ta sanar da aiwatar da shari'a

Sarkin Beunei, Sultan Hassanal Bolkiah
Image caption Kashi biyu cikin uku na al'ummar Brunei 420, 000 Musulmi ne

Masarautar Brunei ta sanar da cewa za ta fara aiwatar da wasu dokokin addinin Musulunci masu tsauri, karkashin sabuwar doka.

Dokokin wadnda za su shafi Musulmin kasar kadai, sun hada da jefe ma'auratan da suka yi zina da yanke hannun barayi da dukan masu shan giya ko wacce ta zubar da ciki.

Nan da wata shida sababbin dokokin za su fara aiki.

Da ma can an hana sayar wa ko shan giya, a kasar dake amfani da dokokin addinin Musulunci fiye da makotanta Malaysia da Indonesia.

Brunei na daga cikin kasashen nahiyar Asia dake da matukar tsadar rayuwa, saboda arzikin mai da kuma iskar gas, amma ilimi da kiwon lafiya kyauta ne ga 'yan kasar.