Matsalar take hakkin bil adama a China

Image caption Shugaba Xi Jinping na China

Wasu jami'an majalisar dinkin duniya sun soki yadda hakkin bil adama ke tabarbarewa a China suna masu nuna damuwa dangane da kama 'yan adawa.

Sannan kuma zargin azabtar da wadanda suke zaman gidan kaso, da kuma ci gaba da amfani da tsarin nan na hukuncin kisa.

Jami'an majalisar dinkin duniyar sun bayyana hakan ne yayin taro a birnin Geneva a kan hakkin bil adama.

Amma wani jami'in diplomasiyyar Chinan, ya amince cewa kasar na fuskantar kalubale ta fuskar inganta kare hakkin bil adama:

Wakiliyar BBC ta ce "koda a wajen da ake taron wasu musulmi 'yan kabilar Wigu na Chinar sun yi ta ihu suna Allah wadai da yadda hukumomin China suke take hakkin bil adama".

Karin bayani