Hotuna masu tayar da hankali a Facebook

Image caption Facebook ya ce zai yi gargadi ga masu son kallon hotunan tayar da hankali

Shafin Facebook ya sake bai wa masu amfani da shi damar sanya hotuna masu tayar da hankali --- wadanda suka hada da bidiyon da za su nuna mutum ana fille masa kai -- a shafin.

A watan Mayu ne shafin ya dakatar da wallafa hotunan da ke tayar da hankali bayan masu amfani da shi sun koka kan cewa hotunan na firgitar da su.

Sai dai a yanzu shafin ya ce ya kamata masu hulda da shi su yi zabi kan ko za su kalli hotunan ko kuma su yi suka ga wadanda suka sanya irinsu a manhajarsa.

Facebook ya kara da cewa koda yake zai bari a rika sanya hotuna masu tayar da hankali amma zai yi gargadi ga masu son kallon hotunan domin su sani cewa abin da za su kalla ka iya yi musu illa.

Bai kamata ba

Masana harkokin sada zumunta dai sun ce sanya hotunan da ke tayar da hankali a Facebook zai yi matukar illa ga tunanin masu amfani da shi.

Shi ma Firai Ministan Birtaniya, David Cameron, ya soki matakin, yana mai cewa hakan rashin sanin ya kamata ne.

Wani sako da ya aike ta sahfinsa ta Twitter, Mista Cameron, ya ce: ''Rashin ya kamata ne idan Facebook ya wallafa hotunan mutum idan ana sare kansa, ba tare da yin gargadi ga masu hulda da shi ba. Dole ne su yi wa mutane bayanin dalilin da zai sa su yi hakan''.

Karin bayani