An kori 'yan majalisar dokokin India su 2

Image caption Lalu Prasad Yadav, daya daga cikin 'yan majalisar da aka kora

A India an kori wasu manyan 'yan siyasa biyu daga majalisar dokokin kasar, bayan kotu ta same su da laifin cin hanci da rashawa.

Mutanen biyu sune; Lalu Prasad Yadav, wani tsohon minista, da kuma wani dan siyasar, Jagdish Sharma.

Kotun ta yanke masu hukuncin daurin shekaru biyar.

Wannan matakin dai ya zo ne bayan kotun kolin kasar ta yanke cewa ba wata rigar kariya da za ta hana a kori duk dan majalisar da aka kama da laifi.

Karin bayani