Nokia ya kaddamar da sabbin wayoyi

Image caption Sabbin wayoyin Phablet da kuma Tablet

Nokia ya fitar da sabbin wayoyin hannu masu girma da ake kira "phablets" da kuma sabon allon komfutar hannu wato "tablet ".

Sabuwar wayar tana daukar hotuna masu inganci kuma rangadau.

Phablets din na amfani da massarafar 4G don sarrafa bayanai ba kamar komfutar hannu ta Surface 2 ba wacce kamfanin Microsoft ya kaddamar.

An yi bukin kaddamar da sabbin wayoyinne a Abu Dhabi.

Daga farkon badi ne, Nokia zai koma hannun Microsoft bayan sun cimma yarjejeniyar cefenar da Nokia a kan dala biliyan bakwai da dubu dari hudu.

Ana kallon matakin Nokia din a matsayin kokarin goggawa da wayoyin Apple da Samsung.

Karin bayani