Saudiyya za ta hukunta wasu mahajjata

Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta bukaci a dauki tsauraran matakai a kan 'yan kasar da suka yi aikin hajjin bana ba tare da neman izinin hukuma ba.

Ma'aikatar ta kuma bukaci a hukunta 'yan kasashen waje dake aiki da Saudiyya wadanda suma suka saba ka'ida.

Rahotanni a kafafen yada labaran Saudiyya sun ce ma'aikatar ta aikewa gwamnonin larduna wasiku don su nemi mutane dubu 120 da suka yi aikin hajjin bana ba tare da izinin hukuma ba.

An baiwa mutanen sammacin sun bayyana ofishin 'yan sanda a ranar Lahadi.

Za a ci tarar 'yan Saudiyyar da aka kama da wannan laifin, a yayinda 'yan kasashen waje za a iya tasa keyarsu zuwa gida tare da haramta musu shiga kasar na tsawon shekaru 10.

Karin bayani